Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{a.s} - ABNA : Yayi wannan bayanin ne jin kadan bayan da gwamnatin Amurka ta sanar da cewa nan ba da jimawa ba za’a sake yi wa Amurkawa Karin rigakafin kamuwa da cutar Korona, ya tabbatar cewa babu wasu dalilai a Kimiyance da ke nuna cewa a kwai bukatar Karin yin Allura adaidai lokacin da wasu da dama suke jira a yi musu ko da sau guda.
Ana sa bangaren shugaban hukumar lafiya ta duniya Tedros Adhanom ya bayyana cewa rashin nuna Adalci kan rigakafin abin kunya ne ga dukkan dan Adam, kuma idan baa tsaya an magance cutar tare ba, to za’a kara tsawaita yaduwar Annobar a tsawon shekaru, abin da za’a iya shawo kanta cikin watanni idan aka yi aiki tare.
342/